Kungiyar "Amnesty Internationl" Ta Bukaci A Daina Syarwa Da Saudiyya Makamai.
A daina Sayarwa da Kasar Saudiyya Makamai
Kungiyar kare hakkin bil'adam ta "Amnesty International" ta kirayi Amurka da Birtaniya da su dakatar da sayarwa kasar Saudiyya Makamai.
A yau talata ne dai, kungiyar kare hakkin bil'adaman ta "Amnesty International' ta bayyana bukatarta na ganin cewa; Kasashen Amurka da Birtaniya sun dakatar da sayarwa Saudiyya makamai da gaggawa, domin tana amfani da su akan kasar Yamen.
Bugu da kari, kungiyar ta kare hakkin bil'adaman ta bukaci da a kafa kwamitin bincike na kasa da kasa domin hukunta wadanda su ke da hannu a shelanta yaki akan kasar Yamen wanda ya sabawa doka.
Shugaban kungiyar ta Amnesty International a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka, Phillipe Loter ya ce; Abin kunya ne a ce wasu kasashe suna sayarwa da kawancen Saudiyya makamai.
A cikin watan Maris na 2015 ne Saudiyya da kawayenta su ka shelanta yaki a kan al'ummar Yamen wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.