Dec 10, 2018 10:03 UTC
  • Amnesty Ta Bukaci ICC Ta Binciki Kisan-kiyashin Da Boko Haram Ta Aikata

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International, ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta duniya cewa da ICC, tada binciki lamarin kisan-kiyashin da kungiyar Boko ta aikata tun bayan kafuwarta.

A rahoton data fitar mai shafuka 74 kungiyar ta Amnesty ta zargi Najeriya da kasa gurfanar da wadanda keda hannu a ayyukan na Boko Haram gaban kotu.

Saidai a wani rahoto data fitar a ranar 5 ga watan Disamba, mai shigar da kara ta kotun ta ICC, Fatou Bensouda, ta ce Najeriya ta dauki kwararen matakai domin binciken lamarin.

Tun dai bayan bullansa a 2009, rikicin Boko haram ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 27,000 tare da tilasta wa wasu Miliyan 1,8 kaurace wa muhallensu a arewa maso gabashin Najeriya, wanda kuma ya haddasa tabarbarewar al'amurran jin kai a yankin tafkin Chadi.

 

Tags