Masar ta dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakaninta da Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12424-masar_ta_dakatar_da_zirga_zirgar_jiragen_tsakaninta_da_saudiyya
An dakatar da zirga-zirgar jirage
(last modified 2018-08-22T06:59:05+00:00 )
Oct 14, 2016 02:15 UTC
  • Masar ta dakatar da zirga-zirgar jiragen tsakaninta da Saudiyya

An dakatar da zirga-zirgar jirage

Kamfanin dillancin labarun Anatoly na kasar Turkiya, ya ambato cewa; Kamfanonin yawon bude ido na kasar Masar sun sanar a jiya alhamis cewa; Ta jingine dukkanin zirga-zirgar masu zuwa umrah, Saudiyya har illa ma sha Allahu.

Matakin na kamfanonin yawon bude-idon na kasar Masar, ya ce; dalilin yin haka shi ne kara kudin fito da kuma na izinin shiga da fice da Saudiyyar ta karawa 'yan kasar waje.

Saudiyyar dai ta kara kudin samun izinin shiga kasar zuwa dalar Amurka 533.

Masar din dai ta zama kasar farko da ta jingine zirga-zirgar maniyyata zuwa saudiyyar saboda kara kudin samun izinin shiga.