Jami'ar Azhar: Yakin Siriya, Ba Yakin Sunna Da Shi'a Ba Ne
Shugaban Jami'ar al-Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmad Tayyib yayi watsi da kokarin da wasu kasashen larabawa suke yi na bayyana yakin da ke gudana a kasar Siriya da cewa yaki ne tsakanin Sunna Da Shi'a, inda ya ce ko da wasa ba haka lamarin yake ba.
Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a ziyarar da ya kai Cibiyar binciken Alkur'ani mai girma da ke birnin Jakarta, babban birnin kasar Indonusiya inda ya ce sabanin abin da wasu suke yadawa, yakin da ke gudana a kasar Siriya ba yaki ne tsakanin Sunna da Shi'a ba.
Shehin Jami'ar ta Al-Azhar ya kara da cewa 'yan Shi'a da Sunna 'yan'uwan juna ne, kuma tsawon tarihi sun kasance 'yan'uwan juna, don haka sai ya bukaci samun karin dankon zumunci tsakanin mabiya wadannan mazhabobi biyu da kuma wajibcin haramta zubar da jinin junansu.
A baya-bayan nan dai wasu kasashen larabawa musamman kasar Saudiyya tare da haramtacciyar kasar Isra'ila suna ci gaba da kokari wajen bayyana yakin da ke gudana a Siriyan a matsayin yaki tsakanin Sunna da Shi'a don cimma manufarsu ta gwara kan musulmi