Masar: An Kashe Wani Babban Jami'in Sojan Kasar Masar.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i12793-masar_an_kashe_wani_babban_jami'in_sojan_kasar_masar.
Kisan Gillar Kwamadan Sojan Tankokin Yakin Masar
(last modified 2018-08-22T06:59:07+00:00 )
Oct 22, 2016 15:25 UTC
  • Masar: An Kashe Wani Babban Jami'in Sojan Kasar Masar.

Kisan Gillar Kwamadan Sojan Tankokin Yakin Masar

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato majiyar tsaron Masar na cewa; Da safiyar yau asabar ne wasu 'yan bindiga su ka harbe Janar Adil Raja'i, wanda shi ne kwamandan Rundunar tankokin yaki na kasar, a lokaci da ya ke fitowa daga gidansa.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kisan.

Kasar Masar dai ta bude yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda da su ke da matsuguni a yankin Sina.

A karshen watan da ya shude wasu masu dauke da makamai sun kashe sojojin Masar 12  a shingen bincike da ke gundumar Sina ta arewa.