Zanga-zangar Mutanen Bahrain Domin Kare Sheikh Isa Qassim
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13060-zanga_zangar_mutanen_bahrain_domin_kare_sheikh_isa_qassim
Dubban Mutanen Kasar Baharain sun yi Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Sheik Isa Qasim.
(last modified 2018-08-22T06:59:09+00:00 )
Oct 28, 2016 15:30 UTC
  • Zanga-zangar Mutanen Bahrain Domin Kare Sheikh Isa Qassim

Dubban Mutanen Kasar Baharain sun yi Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Sheik Isa Qasim.

Dubban Mutanen Kasar Baharain sun yi Zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Sheik Isa  Qasim.

Tashar Telbijin din Lu'u,lulah ta 'yan adawar kasar Bahrain, ta bada labarin cewa; A yau juma'a dubban mutanen kasar sun gudanar da zanga-zanga a yankunan kasar daban-daban, suna masu neman a janye raba babban malamin addinin kasar da hakkin zaman dan kasa.

Masu zanga-zangar sun rika bada taken kiran mahukuntan kasar da su saki fursunonin siyasa.

Bugu da kari wasu mutanen kasar sun yi zaman dirshan a bakin gidan shehun malamin a matsayin bashi kariya daga mahukuntan kasar.

Tun a cikin watan Rebrairu na 2011 ne dai al'ummar kasar ta Bahrain su ka fara yunkurin neman samar da sauye-sauye a cikin kasar.