Gargadi Dangane Da Makomar Masallacin Qudus
Majalisar Koli Ta Fatawa A Palasdinu ta yi gargadi akan yiyuwar rushe masallacin Qudus.
Cibiyar Tattara Bayanai ta Palasdinu ta ce; Ramukan da 'yan sahayoniya su ke hakawa a karkashin masallcin Qudus, yana yin barazana ga rushewarsa.
Cibiyar ta ci gaba da cewa; Wajibi ne ga al'ummar musulmi da su farka daga bacci domin yin aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa na kare alqiblar farko ta musulmi kuma wurin da manzon Allah (s.a.w.a) ya yi mi'iraji.
Yahudawa, 'yan share wuri zauna na kai kutsawa cikin mallacin na Qudus, bisa cikakkiyar kariyar jami'an tsaron haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Makwanni biyu da su ka wuce ne dai hukumar kare wuraren tarihi ta majalisar dinkin duniya, "Unesco" ta ce; Yahudawa ba su da tarihi a cikin birnin na Qudus ko kadan.