Masar: Fararen Hula A Harin Sojojin Masar A Sina
Nov 09, 2016 15:55 UTC
Sojojin Masar Sun kashe fararen hula da dama a wani hari da yankin Sinaa ta arewa.
A wani hari da manyan bindigogi da sojojin masar din su ka kai a yanin al-mu'ainah da ke gabacin garin Abu Dhuwailah, da hakan ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.
Shedun ganin ido sun ce an bar gawawwakin mutane da dama a cikin gidajensu, ba tare da an yi dauko su domin yi musu jana'iza ba.
Masar tana fada da ayyukan ta'addanci ne a cikin yakin na Sinaa da kungiyoyi irin Ansaru baitul muqaddas su ke da sansani.
Makwanni biyu da su ka gabata ma dai an kashe wani janar na kasar da shi ne kwamandan rundunar tankokin yakin kasar a kofar gidansa da ke kusa da birnin alqahira.
Tags