Kasashen Masar Da Iraki Sun Kama Hanyar Karfafa Alaka A Tsakaninsu
A daidai lokacin da alaka tsakanin kasashen Masar da Saudiyya ta yi kamari, a gefe guda kuma kasashen Masar da Iraki sun kama hanyar bunkasa alaka a tsakaninsu, sakamakon haka ministan makamashi na kasar Iraki Qasim Fahdawai ya kai ziyarar aiki zuwa Masar inda ya gana da shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi a ranar Lahadin da ta gabata.
A ziyarar aikin da ministan makamashin kasar Iraki Qasim Fahdawi ya kai zuwa kasar Masar a ranar Lahadi 13 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki ya gana da shugaban kasar ta Masar Abdul-Fatah Al-Sisi a birnin Alkahira, inda suka tattauna batun hanyoyin karfafa alaka da taimakekkeniya a bangarori da dama a tsakanin kasashensu.
A shekarun baya dai kasashen Masar da Iraki suna daga cikin manyan kasashen Larabawa hudu masu karfin fada a ji a tsakanin kasashen Larabawa, inda a wancan lokaci kasashen Saudiyya, Siriya, Masar da Iraki suke juya akalar kasashen Larabawa kafin rikicin siyasa ya tarwatsa kansu wasu daga cikin kasashen suka shiga cikin halin ni 'ya su. Sai dai a halin yanzu haka matakin karfafa alaka a tsakanin kasashen Masar da Iraki lamari ne da zai yi gagarumin tasiri a fagen siyasar yankin gabas ta tsakiya.
Tun daga lokacin da kasar Iraki ta shiga cikin halin dambaruwar siyasa da bullar tashe-tashen hankula sakamakon tsoma bakin manyan kasashen duniya a harkokin cikin gidan kasar, matsayin kasar Masar a fili yake kan kasar ta Iraki, inda a kullum take jaddada matsayinta na ganin kasar ta ci gaba da zama kasa daya dunkulalliya tare da neman kawo karshen tsoma bakin kasashen waje a harkokin siyasar cikin gidan kasar ta Iraki.
A gefe guda kuma kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen Masar da Saudiyya da take daukan kanta a matsayin jagorar kasashen Larabawa a wannan lokaci, alakar ta fara fuskantar matsala ce sakamakon matakin da kasar Masar ta dauka na goyon bayan shirin kasar Rasha na kokarin shawo kan rikicin kasar Siriya lamarin da ya fusata masarautar Saudiyya har ta janye jakadarta daga Masar tare da dakatar da aikin kamfaninta na Aramco da ke tura man fetur zuwa kasar Masar.
Tuni dama kasashen Masar da Iraki suna kokarin kyautata alaka a tsakaninsu amma wannan sabani da ya kunno kai a tsakanin Masar da Saudiyya ya kara hanzarta matakan kyautata alakar kasashen na Iraki da Masar, kuma a zantawar da ta gudana a tsakanin fira ministan Iraki Haidar Abadi da shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ta hanyar wayar tarho, fira ministan Iraki ya bayyana shirin kasarsa na wadata Masar da man fetur din da take bukata.
Har ila yau ziyarar aikin da ministan makamashin kasar Iraki ya kai zuwa Masar tare da ganawa da shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi a ranar Lahadin da ta gabata, ta biyo bayan ziyarar aikin da ministan man fetur da albarkatun kasar Masar ya kai zuwa kasar Iraki ce a farkon wannan wata na Nuwamba, kuma kasashen biyu sun jaddada bukatar bunkasa alaka a bangarori da dama a tsakaninsu musamman a fuskar makamashi.
A bangare guda kuma a daidai lokacin da kasashen Masar da Iraki suka kama hanyar karfafa alaka a tsakaninsu, wasu rahotonni sun bayyana cewa: Muhammad bin Zayad Ali-Nahyan yarima mai jiran gadon sarautar garin Abu-Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya gana da shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi domin shiga tsakani a sabanin da ke tsakanin Masar da Saudiyya, inda shugaba Al-Sisi ya gindaya sharadin sake kyautata alaka da Saudiyya da cewa; sai sarkin Saudiyya da kansa ya bada hakuri ga kasar Masar.