Palasdinu: Sojojin Yahudawa Sun Jikkata Palasdinawa Biyu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i13951-palasdinu_sojojin_yahudawa_sun_jikkata_palasdinawa_biyu
An jikkata Palasdinawa Biyu A harbin da aka yi musu
(last modified 2018-08-22T11:29:15+00:00 )
Nov 16, 2016 07:00 UTC
  • Palasdinu: Sojojin Yahudawa Sun Jikkata Palasdinawa Biyu

An jikkata Palasdinawa Biyu A harbin da aka yi musu

Tashar telbijin din al-alam, watsa shirye-shiryenta daga nan Tehran, ta ce; sojojin na yan sahayoniya sun bude wuta akan Palasdinawa a birnin Ramalla da ke yammacin kogin jordan.

Kawo ya zuwa yanzu dai an tabbatar da jikkatar Palasdinawa biyu, yayin da sojojin na yahudawan sahayoniya su ka yi awon gaba da wasu palasdinawa biyu.

Babu wani dalili na kai harin ko kuma kame Palasdinawa da 'yan sahayoniya su ka yi.

Yankin Ramallah dai shi ne cibiyar gwamnatin kwarya-kwaryar palasdinu, sai dai duk da haka 'yan sahayoniyar na yi masa kutse da duk lokacin da su ka ga dama.