Yiyuwar Kyautatuwar Alaka Tsakanin Gwamnatin Masar Da Kungiyar Ihwan Ta Kasar
Gagarumin canje-canjen da ake samu a fagen siyasa da na shari'a a kasar Masar lamari ne da ke nuni da cewa: Akwai yiyuwar samun kyautatuwar alaka tsakanin gwamnatin Masar da kungiyar Ihwanul-Muslim ta Muslim Brotherhood ta kasar.
A jawabin da ya gabatar a gaban kotu a yayin gudanar da shari'arsa a ranar Alhamis 24 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki: Muhammad Baltaji daya daga cikin shugabannin kungiyar Ihwanul-Muslimin ta 'yan uwa musulmi a kasar Masar ya jaddada cewa; Kungiyarsu ta Ihwan bata da wata alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda da suke kai hare-haren wuce gona da iri a kasar, kuma sabaninsu da gwamnatin Masar sabani ne irin da mahangar siyasa.
Hakika kyautatuwar alaka tsakanin gwamnatin Masar da kungiyar Ihwan lamari ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Masar amma a fili yake cewa alakar tana da gagarumin tasiri a fagen siyasar yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda bullar tabarbarewar alaka tsakanin bangarorin biyu a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan ta yi mummunan tasiri a fagen siyasar kasashen yankin gabas ta tsakiya.
A tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2014 kungiyar Ihwan ita ce babbar mai taka rawa a fagen siyasar Masar, inda ta lashe zabukan 'yan Majalisun Dokokin Kasar a shekara ta 2012, sannan a yayin da Muhammad Morsi na kungiyar Ihwan ya tsaya takarar shugabancin kasa, mafi yawan kasashen Larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiyya sun dauki matakin marawa Ahmad Shafiq baya ne amma duk da haka Morsi ya samu nasarar lashe zaben.
Har ila yau a bayan da Muhammad Morsi ya dare kan karagar shugabancin kasar ta hanyar tsarin dimokaradiyya, kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun dauki matakin hada kai da sojojin kasar ta Masar domin ganin bayan gwamnatin Masar, inda a karshe sojojin karkashin jagorancin Abdul-Fatah Al-Sisi suka kifar da gwamnatin 'yan Ihwan ta Muhammad Morsi a shekara ta 2013.
Bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi a Masar, manyan kasashen Larabawa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Kuwait sun gabatar da taimakon miliyoyin dalolin Amurka ga gwamnatin Masar tare da bukatarta kan ta sanya kungiyar Ihwanul-Muslimin cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda da nufin samun saukin murkushe kungiyar Ihwan daga kan doron kasa, inda mahukuntan Masar suka dinga gurfanar da 'yan kungiyar Ihwan a gaban kotu ana yanke musu hukunce-hukunce da suka hada da na kisa, daurin rai da rai da kuma na zaman shekaru a gidajen kurkuku.
A cikin 'yan watannin baya-bayan nan da aka samu bullar sabani a tsakanin kasashen Saudiyya da Masar da ta kai ga Saudiyya ta janye jakadanta daga Masar tare da dakatar da gabatar mata da tallafi, hakan ya zame wata babbar dama ga gwamnatin Masar da kungiyar Ihwan na kyautata alakar da ke tsakaninsu da nufin gina kasarsu baki daya nesa da tsoma bakin kasashen waje.