Masar: Fashewar Wasu Abubuwa Sun Kashe mutane 6 A Birnin Alkahira.
Dec 09, 2016 08:29 UTC
An Kashe Mutane Shida A Wani Hari A Birnin Alkahira.
Tashar telbijin din gwamnatin Masar ta ce; wasu abubuwa sun fashe a kusa da wata cibiyar bincike na tsaro da ke birnin alqahira.
Tashar telbijin Nile ta ce abubuwan sun fashe ne a unguwar Talibiyyah da ke cikin babban birnin.
Majiyar yan sanda ta ce; fashewar ta faru ne a dan da wurin binciken tsaro a kusa da wani masallaci.
Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan wadanda su ka kai harin, da kuma girman barnar da ya yi.
Tags