Mutanen Bahrain Sun Kona Tutar Isra’ila A Kasar
Dubban mutanen kasar Bahrain ne suka gudanar da gangami a unguwar Diraz da ke gefen birnin Manama, domin yin Allawadai da ziyarar tawagar Isra’ila a kasar.
Jaridar yanar gizo ta Manama Post ta habarta cewa, dubban mutanen sun taru ne a kofar gidan babban malamin addinin muslunci na kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim.
Masu gangamin sun yi ta rera take yin Allawadai da masarautar Alkhalifah, kan yadda ta tarbi tawagar yahudawan sahyuniya daga Isra’ila, tare da bude sabon shafin kyakkayawar alaka a bayyane tare da Isra’ila, wanda hakan yake a matsayin cin zarafi ga dukkanin al’ummar kasar Bahrain, wadanda ba su amince da hakan ba.
Haka nan kuma masu gangamin sun kona tutar haratacciyar kasar Isra’ila a wurin, a wata alama da ke nuni da cewa kulla alaka tsakanin Bahrain da Isra’ila ba da yawun al’ummar kasar ne ba.
Masarautar Bahrain dai na daga cikin masarautun larabawa da suke da kyakkyawar alaka da Isra’ila a boye, inda Isra’ila ke ba gwamnatin Bahrain gudunmawa wajen murkushe ‘yan adawar siyasa a kasar, da kuma kayan azabtar da su a gidajen kurkuku na kasar.