Bahrain: An Bude Sabon Shafi A Gwagwarmayar Al'umma
Bayan kisan fursunonin siyasa 3 a kasar Bahrain zan bude wani sabon shafi na gwgawarmaya.
Wata majiyar 'yan kasar Bahrain masu fafutuka ta : Harkatul Wa'fa al-islamy' ta ce; Bayan kisan da aka yi wa matasa uku masu fafutukar siyasa a kasar,an bude wani sabon shafi na gwagwarmaya a kasar.
Daya daga cikin jami'an kungiyar Murtadha al-Sindy, ya fada a yau cewa; Yunkurin al'ummar kasar na ruwan sanyi, babu abinda ya jawo wa al'ummar kasar sai karin zalunci, don haka yanzu an shiga wani sabon shafi na daukar makamai.
Murtadha al-Sindy ya ci gaba da cewa; Sun gama shiryawa tsaf, domin daukar makamai da yin gwagwarmaya da jihadi.
A ranar lahadin da ta gabata ne dai mahukuntan Bahrain su ka zartar da hukuncin kisa akan wasu matasa uku da su ne Sami Mushaimah, da Ali Sankis da Abbas Sumai'i. Tun a 2014 ne aka kame su a yankin al-Dayah tare da tuhumarsu da kai harin bom.
Jim kadan bayan kashe su, kasar ta Bahrain ta tsunduma cikin zanga-zanga da bore a sassa daban-daban.