Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Soki Isra'ila Kan Mamayar Palestinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17417-kungiyar_kasashen_larabawa_ta_soki_isra'ila_kan_mamayar_palestinu
Kungiyar kasashen larabawa ta soki matakin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila kan ci gaba da abunda ta kira satar filayen Palestinawa.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Feb 07, 2017 08:52 UTC
  • Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Soki Isra'ila Kan Mamayar Palestinu

Kungiyar kasashen larabawa ta soki matakin mahukuntan yahudawan mamaya na Isra'ila kan ci gaba da abunda ta kira satar filayen Palestinawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan amuncewa da majalisa Israila ta yi na ci gaba da mallakar daririwan hektoci na filaye al'ummar Palestinu.

A wata hira da kanfanin dilnacin labaren AFP, babban sakataren kungiyar Ahmed Aboul Gheit cewa wannan zaluncin na Isra'ila akan al'ummar Palestinu zai maida hannun ogogo baya a yunkurin samar da zamen lafiya da inttatun kasashe biyu da aka dade ana fata.

Ita ma dai a nata bangare masarautar Jodan tayi Allah-wadai da wannan matakin wanda a cewarta na tsokana ne wanda kuma zai kawo karshen duk wani tsammani na samun kasashe biyu masu cin gashin kansu a yankin.