Gwamnatin Masar Ta Bayyana Shirinta Na Karfafa Rundunar Sojin Kasar Lebanon
Shugaban Masar ya bayyana shirin kasarsa na taimakawa kasar Lebanon a fagen karfafa rundunar sojinta.
A taron menema labarai da shugabannin kasashen Masar da Lebanon suka gudanar a tsakaninsu a birnin Alkahira a yau Litinin: Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ya bayyana shirin kasarsa na taimakawa a fagen karfafa rundunar sojin Lebanon da hukumar tsaron kasar a karkashin yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fagen yaki da ayyukan ta'addanci.
Abdul-Fatah Al-Sisi ya yi furuci da cewa: Lebanon kasa ce 'yantacciya da take da karfi tare da muhimmanci a yankin gabas ta tsakiya, don haka Masar tana nan a kan matsayinta na ci gaba da goyon bayan kasar ta Lebanon.
A nashi bangaren shugaban kasar Lebanon Michel Aun ya jaddada muhimmancin kasar Masar a fagen yaki da ayyukan ta'addanci tare da jaddada matakin karfafa ayyukan kwamitin kolin hadin gwiwa a tsakanin kasarsa da Masar domin cimma manufar samar da kwamitin. Kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka tattauna matsalolin tsaro musamman ayyukan ta'addanci da suke ci gaba da addabar yankin gabas ta tsakiya.