Isra'ila Ta Janye Jakadanta A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i17664-isra'ila_ta_janye_jakadanta_a_masar
Gwamnatin Yahudawan mamaya na Isra'ila ta sanar da janye jakadanta na wani dan lokaci a birnin Alkahira na kasar Masar saboda dalilai na tsaro.
(last modified 2018-08-22T06:59:41+00:00 )
Feb 15, 2017 02:22 UTC
  • Isra'ila Ta Janye Jakadanta A Masar

Gwamnatin Yahudawan mamaya na Isra'ila ta sanar da janye jakadanta na wani dan lokaci a birnin Alkahira na kasar Masar saboda dalilai na tsaro.

A cikin wata sanarwa data fitar hukumar leken asiri Isra'ilar ta ce saboda dalilai na tsaro jami'an diflomatsiyanta ba zasu koma birnin Alkahira ba, saidai ba tare da yin karin haske ba ko tun yaushe ne jami'an Isra'ilar suka fice daga kasar ta Masar ba. 

Amma jaridar ''The  Telegraph'' ta Biritaniya data fara kawo labarin a Jiya Talata, ta ce jakadan Isra'ilar, David Govrin, na a Isra'ila tun a karshen shekara 2016 data gabata. 

Isra'ila dai ta bude offishin jakadancinta a Masar ne tun a watan Satumba 2015 shekaru hudu bayan da masu zanga-zanga suka farmawa offishin nata, a ranar 9 ga watan Satumba da kuma ta cilasta mata kwashe jami'anta.

Masar dai ita ce kasar Larabawa ta farko cikin biyu kalas da ake dasu kawo yanzu da ya hada Jodan wadanda suka cimma yarjejeniyar zamen lafiya da Isra'ila.