Dariruwan Yahudawan Sahayina sun kai farmaki kan Masallacin Aksa
Dariruwan Yahudawa 'yan kama guri zauna tare da goyon bayan Dakarun HKI sun kai farmaki kan Masallacin Aksa tare da hana Palastinawa shiga cikin Masallacin.
Tashar telbijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a wannan Laraba manyan motoci masu rusa gine-gine da ake kira da Bulldozers na HKI sun rusa gidajen Palastinawa da dama a garin Isawiyah dake arewacin Baitul Makdis, sannan kuma sun rabawa wasu iyalai takardar galgadi na su tattara yana su yana su su bar gidajen domin za a rusa su.
Muhamad Abu Hums Shugaban Kwamitin bibiyar halin da garin Isawiyah ke ciki ya ce a yayin raba takardar galgadin saida suka rusa gidan wani Palastine guda bayan da suka ci zarafinsa shi da iyalan sa.
Yahudawan na Sahawuna na kokarin gina wani katafaran gini na Sinima a kusa da Baitul-Makdis, kuma a yunkurin da suke na korar Palastinawa daga yankin sun haramta musu shiga tsakiyar garin kan da'awar harakokin tsaro.