An Soki Gwamnatin Kasar Bahrain Kan Cin Zarafin Fararen Hula
(last modified Fri, 24 Feb 2017 12:36:50 GMT )
Feb 24, 2017 12:36 UTC
  • An Soki Gwamnatin Kasar Bahrain Kan Cin Zarafin Fararen Hula

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa ta soki lamirin masarautar kasar Bahrain kan cin zarafin fararen hula masu fafutuka ta siyasa a kasar.

Babban jami'in gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa a yankin gabas ta tsakiya Joe Storck ya bayyana cewa, shirin da masarautar Bahrain take da shin a gurfanar da fararen hula da 'yan adawar siyasa  agaban kotunan soji ya yi hannun riga da dukkanin dikoki na kasa da kasa, tare da bayyana hakana matsayin wani nau'in mulki na kama karya  akan al'ummar kasar.

A cikin bayanin da kungiyar ta fitar a jiya, ta bayyana cewa akwai abubuwa da dama da suka farua  kasar ta Bahrain na keta hurumin bil adama, saboda dalilai na siyasa da kuma banbancin mazhaba, wanda mahukuntan kasar sun ki su amince jami'an kare hakkin bil adama su gudanar da bincike a kan lamarin.

Ko a kwanakin baya dai masautar ta kasha wasu masu fafutuka 3 bisa tuhumar cewa suna da hannu wajen kasha wani jami'in 'yan sanda na kasar hadaddiyar daular larabawa, a kasa da makonni biyu da suka gabata ma masarautar kasar ta kasha matasa hudu har lahira ba tare da wani dalili ba, sai domin suna adawa salon mulkin kama karya na kasar.