Isra'ila Ta Hana Wani Mai Kare Hakkin Bil Adama Shiga Palastinu
Mar 03, 2017 03:13 UTC
Haramtacciyar kasar Isra'ila ta hana wani babban jami'i mai sanya ido kan hakkokin bil adama na kasa da kasa shiga Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, jami'an haramtacciyar kasar Isra'ila sun hana bayar da izinin shiga cikin yankin Palastinu da suka mamaye ga Umar shakir, kasantuwarsa daya daga cikin masu sanya ido harkokin Isra'ila na cikin gida.
Tun kafin wanann lokacin Umar Shakir jami'i mai bayar da rahoto kan hakkokin bil adama a kasashen duniya na majalisar dinkin duniya, ya bayyana cewa yana da nufin ziyartar wasu daga cikin yankunan Palastinu domin ganewa idanunsa abubuwan da suke faruwa, amma Isra'ila ta hana shi izinin shiga.
Tags