Masar: An daure'Yan Leken Asirin Isra'ila Zaman Kurkuku Na Har Abada.
Wata kotu a kasar Masar ta daure 'yan leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra'ila, Misrawa da yahudawa zaman kurkuku na har abada.
Wata kotu a kasar Masar ta daure 'yan leken asirin Haramtacciyar Kasar Isra'ila, Misrawa da yahudawa zaman kurkuku na har abada.
Majiyar kotun kasar ta Masar ta sanar a jiya laraba cewa; Wasu Misrawa uku, da 'yan haramtacciyar kasar Isra'ila 6, an yanke musu zaman kurkukun ne na har abada bayan da aka same su da hannu a kan ayyukan ta'addanci.
Mutane biyu da aka yankewa hukuncin a gabansu, wato Audah Talab, Ibrahim Barham, da kuma Salamah Hamad Farhan, Abu Jarad, 'yan kasar ta Masar ne, yayin da sauran kuma basu halarcin zaman kotun ba.
Tun a 2013 ne aka bude shari'ar mutanen da aka tuhuma da leken asirin.