Jami'an Tsaron Isra'ila Sun Kame Wata 'Yar Majalisar Dokokin Palastinu
Jami'an tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame wata 'yar majalisar dokokin Palastinu a yau a gidanta da ke kusa da birnin Alkhalil a gabar yamma da kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labaran shafaqana ya bayar da rahoton cewa, Samira Al Halaiqa 'yar majalisar dokokin Palastinu ce da ke nuna rashina mincewa da zaluncin Isra'ila a kan al'ummar Palastinu, da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da sojojin Isra'ila ke yi.
Rahoton ya ce da jijjifin safiyar yau sojojin Isra'ila sun kai samame a kan gidanta da ke garin Al-shuyukh da ke kusa da birnin Alkhalil, inda suka fitar da ita daga cikin iyalanta, kuma suka da ita wani wuri da ba a sani ba.
Yanzu haka dai 'yan majalisar dokokin Palastinu 10 suke tsare a hannun jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila, da suka hada har da dan majalisa guda daga kungiyar Fatah, da kuma wasu daga kungiyoyin hamas da Jabhat Sha'abiyyah.