Jami'an Tsaron Bahrain Na Ci Gaba Da Kame 'Yan Adawar Siyasa
(last modified Mon, 13 Mar 2017 19:27:21 GMT )
Mar 13, 2017 19:27 UTC
  • Jami'an Tsaron Bahrain Na Ci Gaba Da Kame 'Yan Adawar Siyasa

Jami'an tsaron masarautar Bahrain na ci gaba da kaddamar da farmaki kan gidajen jama'a masu adawar siyasa a kasar tare da kame su.

Shafin yada labarai na Manama Post ya bayar da rahoton cewa, tun da safiyar yau Litinin jami'an tsaron masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain ta fara kai farmaki kan gidajen jama'a  ayankuna daban-daban na kasar, inda suke ta kame mutane ba ji ba gani suna yin awon gaba da su.

Rahoton ya ce a yankin Satra kadai jami'an tsaron sun kame matasa 16 sun yi awon gaba da su ba tare da bayyana wani dalilin yin hakan ba, duk kuwa da cewa hakan ba zai rasa nasaba da dalilai na siyasa da banbancin mazhaba ba.

A cikin makon da ya gabata jami'an tsaron sun kashe wani matashi a lokacin da suka kai farmaki a kan gidajen 'yan adawar siyasa a kusa da birnin Manama, inda  akuma suka dawo suka kame dukkanin 'yan uwansa 4 da kuma wasu daga cikin danginsa.