Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila Sun Kai Farmaki Kan Palasdinawa
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan jami'ar Qudus da ke yankin Abu-dis a garin Baitu-Maqdis, inda suka jikkata dalibai masu yawa.
Majiyar watsa labaran Palasdinu ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmakin wuce gona da iri kan jami'ar Qudus a yau Laraba, inda suka fuskanci mai da martani daga dalibai lamarin da ya janyo jikkatan Palasdinawa masu yawa sakamakon harbinsu da bindiga.
Har ila yau sojojin haramtacciyar kasar ta Isra'ila sun harba iskar gas mai guba kan daliban lamarin da ya janyo shakewar daliban masu yawa tare da jikkata su.
Kafin kai hari jami'ar ta Qudus sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai samame jami'ar Qudus da ke gabar yammacin kogin Jordan inda suka ci zarafin dalibai Palasdinawa ta hanyar dukansu.