Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada Sakamakon Harbinsa Da Bindiga
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i18782-wani_bapalasdine_ya_yi_shahada_sakamakon_harbinsa_da_bindiga
Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harbe wani bapalasdine har lahira tare da jikkata wasu uku na daban a garin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan.
(last modified 2018-08-22T11:29:51+00:00 )
Mar 24, 2017 05:30 UTC
  • Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada Sakamakon Harbinsa Da Bindiga

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harbe wani bapalasdine har lahira tare da jikkata wasu uku na daban a garin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan.

Kafar watsa labaran Palasdinawa ta Ma'ah ta bada labarin cewa: Gungun sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan yankunan da suke arewacin garin Ramallah a gabar yammacin kogin Jordan a jiya Alhamis, inda suka bude wuta kan wata mota lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar bapalasdine guda tare da jikkata wasu uku na daban.

Kafar watsa labaran ta kara da cewa: Dukkanin Palasdinawan hudu da suke cikin motar matasa ne mazauna sansanin 'yan gudun hijira na Jalizun a garin na Ramallah.

Rahotonni suna bayyana cewa: Daruruwan Palasdinawa ne suka yi shahada tun bayan bullar gwagwarmayar Palasdinawa ta Intifadha a watan Oktoban shekara ta 2015 zuwa yanzu, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da na tsagerun yahudawan sahayoniyya 'yan share wuri zauna ke kai wa kan al'ummar Palasdinu.