Gwamnatin Haramtaciyar Kasar Isra'ila Ita Ce Ke Karfafa Ayyukan Ta'addanci
Ministan watsa labaran kasar Jordan ya bayyana cewa: Ci gaba da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila yana daga cikin dalilan kara karfafa da watsuwan ayyukan ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya.
A ganawarsa da manema labarai a gefen zaman taron sharen fagen zaman shugabannin kasashen Larabawa a kasar Jordan a jiya Litinin: Ministan watsa labaran kasar ta Jordan Muhammad Mu'umini ya bayyana cewa rashin daukan matakan adalci a fagen neman hanyar warware matsalar Palasdinu suna daga cikin muhimman dalilan bullar tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.
Muhammad Mumini ya kara da cewa: Al'ummar Larabawa suna bukatar ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da sulhu musamman ta hanyar warware matsalar Palasdinu cikin adalci da zai kai ga samar da yantacciyar kasar Palasdinu mai cin cikakken gashin kai amma a kullum gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana kokarin ganin ta yi kafar ungulu ga wannan shiri na zaman lafiya da sulhu lamarin da ke kara karfafa habakar ayyukan ta'addanci.
Har ila yau Mu'umini ya jaddada bukatar neman hanyar warware rikicin kasar Siriya ta hanyar lumana.