Jordan: An Bude Taron Kungiyar Kasashen Larabawa A Bahru Mayyit.
(last modified Wed, 29 Mar 2017 12:13:13 GMT )
Mar 29, 2017 12:13 UTC
  • Jordan: An Bude Taron Kungiyar Kasashen Larabawa A Bahru Mayyit.

Sarkin Kasar Jordan ya ce; Babu yadda za a sami zaman lafiya a gabas ta tsakiya ba tare da kafa kasar Palasdinu ba.

Sarkin Kasar Jordan ya ce; Babu yadda za a sami zaman lafiya a gabas ta tsakiya ba tare da kafa kasar Palasdinu ba.

Sarki Abdullah Bin Husain, wanda ya gabatar da jawabin bude taron dazu a yankin Bahru mayyit da ke kasar, ya ce; Babu zaman lafiya, babu kwanciyar hankali a cikin yankin gabas ta tsakiya, matukar ba a sami warware dukkanin batutuwa da su ke da alaka da palasdinu ba, ta hanyar kafa kasashe biyu.

Sarki Abdullah ya ci gaba da cewa; Kasar Isra'ila na ci gaba da gina matsugunan yahudawa yan share wuri zauna da kuma yi wa duk wata dama ta zaman lafiya kafar angulu.

Sarakuna da shugabannin kasashen larabawa suna halartar taron da jordan.