An Tsaurara Matakan Tsaro A Gaza Bayan Kisan Mazin Fuqaha
Dakarun Izzuddin Qssam reshen soji na kungiyar Hamas sun tsaurara matakan tsaroa yankin Zirin gaza baki daya, bayan kisan babban kwamandansu a bangaren ayyukan soji Mazin Fuqaha.
Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, dakarun na Izzaddin Qassam sun sunar da cewa, akwai masu yi wa Isar'ila ayyuka na leken asiria cikin yankin Zirin Gaza, wanda kuma ya zama wajibi su dauki matakan shi kafar wando daya da su.
Yanzu haka dai dakarun na Izzaddin Qassam sun kafa shigayen bincike a wurare daban-daban a ikin dukkanin yankunan zirin Gaza, yayin da Isma'il Haniyyah Firayi ministan Hamas Gaza ya bayyana cewa za su dauki fansa a kan kisan Fuqaha.
A ranar 24 ga watan Maris da ya gabata ne wasu mutane 4 dauke da makamai suka harbe Mazin Fuqaha, babban kwamandan Izzuddin Qassam a bangaren ayyukan soji, inda ya yi shahada ana take.