Bahrain : An Sassautawa Sheikh Ali Hukuncin Zaman Yari
Kotun karya shari'a a Bahrain ta sassauta da shekaru biyar hukuncin zama gidan yari ga jagoran 'yan adawa na kasar dan shi'a nan Sheikh Ali Salmane.
A shekera 2015 ne wata kotu a kasar ta yankewa Sheikh Ali hukuncin zamen gidan kaso na shekara biyar, aman daga bisani kotun daukaka kara ta tsawaita masa hukuncin zuwa shekara tara a shekara 2016 data gabata.
Sheikh Ali Salmane, dan shekaru 51 ana daimasarautar Bahrain tana zarginsa da tada fitina da kuma kin biyaya ga wasu dokoki da suka rataya ga dan kasa, wanda dukkanin zarge-zargen suke da alaka da siyasa da kuma banbancin mazhaba.
Daure Sheikh Ali da kuma soke jam'iyyarsa ta Al-Wefaq da kotu ta yi a shekara 2014 ya janyo zanga-zanga ba kadan ba a wannan kasa ta Bahrain da kuma Allah wadai na wasu kasashen duniya da suka hada da Amurka da Iran da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.