Masar: An Kafa Dokar Ta Baci Bayan Jerin Hare-haren Ta'addanci.
Shugaban kasar Masar ya sanar da kafa dokar ta baci na watanni uku bayan wasu hare-hare da 'yan ta'adda su ka kai wa majami'un kasar a jiya lahadi.
Shugaban kasar Masar ya sanar da kafa dokar ta baci na watanni uku bayan wasu hare-hare da 'yan ta'adda su ka kai wa majami'un kasar a jiya lahadi.
Shugaba Abdulfattah al-sisy ne ya sanar da kafa dokar, jim kadan bayan wasu hare-haren da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta kai a majami'un garuruwan Tanta da Alexadaria. Bugu da kari, shugaban na kasar Masar ya yi kira yi al'ummar Masar din da su ci gaba da bada hadin kai a yaki da ta'addanci a kasar, haka nan kuma ya buka ci duniya da ta kalubalanci masu goyawa ta'addanci baya.
A kalla mutane 46 ne su ka rasa rayukansu wasu fiye da 100 kuma su ka jikkata sanadiyyar hare-haren a cocin al-marqisiyyah da ke Alexadaria da kuma cocin Margirigis da ke garin Tanta.
Shugaban kasar ta Masar ya bukaci sojoji da su tallafawa 'yan sanda wajen bada tsaro ga muhimman cibiyoyin kasar.
Kungiyar Da'esh ta dauki nauyin kai hare-haren biyu.
Kasashen duniya da su kaaada da jamhuriyar musulunci ta Iran sun yi Allah wadai da harin.