Masar: Hizbullah Ba Kungiyar Ta'adda ba ce:
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i1930-masar_hizbullah_ba_kungiyar_ta'adda_ba_ce
Jam'iyyar karamah ta masar ta yi watsi da bayyan Hizbullah a matsayin 'yar ta'adda:
(last modified 2018-08-22T06:57:56+00:00 )
Mar 05, 2016 16:23 UTC
  • Masar: Hizbullah Ba Kungiyar Ta'adda ba ce:

Jam'iyyar karamah ta masar ta yi watsi da bayyan Hizbullah a matsayin 'yar ta'adda:

Tashar telbijin din al-mayadden mai watsa shirye-shiyenta daga Beirut ta watsa wani bayani da jam'iyyar al-Karamah ta Masar ta fitar, da a cikin ta ke yi watsi da matakin kasashen larabawan yankin tekun pasha na bayyana kungiyar Hizbullah a matsayin 'yar ta'adda.

Bayanin ya ci gaba da cewa; sabanin mahangar siyasa bai kamata a ce ya sa an keta hurumi da zubar da mutuncin abokin hamayya ba.

Jam'iyyar ta alkaramah ta ce wajibi ne a rungumi kungiyoyin gwagwarmayar da ake da su a cikin wannan yankin maimakon mayar da su saniyar ware.