Daruruwan Palastinawa A Gidajen Yarin Isra'ila Sun Fara Yajin Cin Abinci
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19508-daruruwan_palastinawa_a_gidajen_yarin_isra'ila_sun_fara_yajin_cin_abinci
Daruruwan Palastinawa da ake tsare da su a gidajen yari daban-daban na haramtacciyar kasar Isra'ila sun fara gudanar da boren yajin cin abinci, wanda shi ne irinsa mafi girma saboda irin mummunan halin da suke ciki.
(last modified 2018-08-22T11:29:58+00:00 )
Apr 17, 2017 10:38 UTC
  • Daruruwan Palastinawa A Gidajen Yarin Isra'ila Sun Fara Yajin Cin Abinci

Daruruwan Palastinawa da ake tsare da su a gidajen yari daban-daban na haramtacciyar kasar Isra'ila sun fara gudanar da boren yajin cin abinci, wanda shi ne irinsa mafi girma saboda irin mummunan halin da suke ciki.

Kungiyar fursunonin Palastinawa ce ta sanar da hakan inda ta ce a yau Litinin kimanin fursunoni 1500 ne suka fara yajin cin abinci sannan kuma ana sa ran adadin zai ci gaba da karuwa har zuwa mutane 2000.

Shugaban kungiyar Fatah Marwan Barghouti wanda shi ma yake tsare a gidan yarin HKI shi ne ya ke jagorantar wannan  yajin cin abincin da aka jima ana tsara shi, don yayi daidai da ranar 17 ga watan Aprilu, wato ranar fursunoni Palastinawa.

Palastinawa dai suna yajin cin abincin ne don nuna rashin amincewarsu da mummunan yanayin da suke ciki a wajajen da ake tsare da su, kamar yadda kuma suke bukatar da a dinga barin iyalansu suna ziyartarsu bugu da kari kan samar musu da hanyar sadarwa da danginsu.