Isra'ila Ta Kai Hari Da Makami Mai Linzami A Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19858-isra'ila_ta_kai_hari_da_makami_mai_linzami_a_syria
Bayanai daga Syria na cewa Israila ta kaiwa kasar wani hari na tsokana da makami mai linzami akan wata barikin soji dake wajen filin jiragen sama na Damascos.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 27, 2017 11:10 UTC
  • Isra'ila Ta Kai Hari Da Makami Mai Linzami A Syria

Bayanai daga Syria na cewa Israila ta kaiwa kasar wani hari na tsokana da makami mai linzami akan wata barikin soji dake wajen filin jiragen sama na Damascos.

Kanfanin dilancin labaren Syria ya rawaito wata majiyar soji na fadan haka tare da cewa harin ya haddasa barna, amman ba mai yawa ba. 

Wannan dai a cewar majiyar ba zai katse masu hamzari ba akan yakin da suke da 'yan ta'adda ba.

Dama kafin hakan tashar Talabijin din Hezbullah ta kasar Lebonon ta rwaito labarin cewa fashewar da akaji a kusa da filin jirgin saman birnin Damascos hari ne na makamai mai linzami daga Isra'ila.