Palasdinawa Na Yajin Aikin gama Gari
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i19862-palasdinawa_na_yajin_aikin_gama_gari
Al'ummar Palasdinu na wani yajin aikin gama gari domin nuna goyan bayansu ga fursunonin dake yajin cin abunci a gidajen kurkukun yahudawan mamaya na Isra'ila.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 27, 2017 11:10 UTC
  • Palasdinawa Na Yajin Aikin gama Gari

Al'ummar Palasdinu na wani yajin aikin gama gari domin nuna goyan bayansu ga fursunonin dake yajin cin abunci a gidajen kurkukun yahudawan mamaya na Isra'ila.

Wakilin kamfanin dilancin labaren AFP ya ce komi ya tsaya cik a birnin Ramallah, inda shaguna na kan tutuna da kasuwani sun kasance a rufe.

Ana sa ran al'ummar ta Palasdinu zasu gudanar da gangami na nuna goyan baya ga fursunoinin su 1,500 dake yajin cin abunci yau kusa da kwanaki 11.

Yanzu haka dai ana cikin zamen dar-dar kasancewar sau tarin yawa irin wannan ganganmin ke karewa a arangama da jami'an tsaron Isra'ila.