Yemen : Jirgin Amurka Marar Direba Ya Hallaka 'Yan Al'Qaida 5
Apr 30, 2017 07:26 UTC
Rahotanni daga Yemen na cewa 'yan ta'ddan Al'Qaida biyar en suka hallaka a yayin da wani jirgin yakin Amurka marar matuki ya kai hari kan motarsu a gabashin birnin Sanaa.
Bayanai daga kasar na cewa an kaiwa motar dake dauke da makamai hari ne da jijibin safiyar wannan Lahadin a lardin Marid dake jihar Al-Jawia a gabashin Sanaa.
Ko a ranar Asabar data gabata ma an hallaka wasu 'yan ta'addan na Al'Qaida uku a wani hari a kudancin kasar ta Yemen.
Tun dai bayan zuwan gwamnatin shugaba Donald Trump, Amurka ta zazafa kai hare-haren ta a kasar ta Yemen dake fama da yaki.
Tags