Kungiyar Hamas Na Shirin Sanar Da Sunan Sabon Shugabanta
(last modified Mon, 01 May 2017 10:52:48 GMT )
May 01, 2017 10:52 UTC
  • Kungiyar Hamas Na Shirin Sanar Da Sunan Sabon Shugabanta

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewar nan da 'yan kwanaki kadan za ta sanar da sunan sabon shugaban kungiyar wanda zai ci gaba da jagorancinta.

Kafafen watsa labaran Palastinun sun jiyo tsohon firayi ministan kasar Palastinun kuma kusa a kungiyar ta Hamas Isma'il Haniya yana fadin hakan inda ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sakamakon zabe na cikin gida da kungiyar ta gudanar don zaben sabbin jami'an kungiyar. 

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya jiyo wani jami'in kungiyar Hamas din da bai ambaci sunansa ba yana cewa za a sanar da sakamakon zaben cikin gidan ne kafin ranar 15 ga watan nan na Mayu da muke ciki.

Wasu majiyoyin dai sun ce daga dukkan alamu shi Isma'il Haniya din ne za a zaba a matsayin sabon shugaban kungiyar wanda idan har ya tabbata to zai maye tsohon shugaban kungiyar Khaled Mash'al wanda a halin yanzu yake zaune a kasar Qatar.