Dakarun Izzudden Al-Qassam Sun Ja Kunnen 'Isra'ila' Kan Batun Fursunoni
Dakarun Izzudden al-Qassam, bangaren soji na kungiyar Hamas ta ba wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila wa'adin sa'oi 24 da amince da bukatun fursunoni masu yajin cin abinci ko kuma su jira abin da zai biyo baya.
Kakakin kungiyar Izzudden al-Qassam din Abu Ubaida ne ya bayyana hakan cikin wani jawabi da kungiyar ta watsa inda ya ce muna jan kunnen makiya (wato yahudawan sahyoniya) da kada su rufe ido kan wadannan halaltattun bukatu na fursunonin. Don haka mun ba wa shugabanninsu sa'oi 24 da su amince da wadannan bukatun.
Abu Ubaida ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ilan da cewa su jira abin da zai faru matukar suka ki amincewa su biya bukatan da fursunonin suka gabatar musu, ba tare da yayi karin haske kan abin da za su yi ba.
Tun ranar 17 ga watan Aprilun da ya gabata ne wasu fursunoni Palastinawa kimanin 1600 da suke gidajen yarin daban-daban na haramtacciyar kasar Isra'ilan suka fara wani yajin cin abinci na har sai baba ta gani matukar dai yahudawan ba su biya musu bukatunsu ba ciki kuwa har da kyautata musu mummunan yanayin da suke ciki da kuma barin 'yan'uwansu su dinga ziyartarsu.