Palasdinu: Isma'ila Haniyya Ya Zama Shugaban Ofishin Siyasa Na Kungiyar Hamas.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20122-palasdinu_isma'ila_haniyya_ya_zama_shugaban_ofishin_siyasa_na_kungiyar_hamas.
A jiya Juma'a ne kungiyar ta Hamas ta zabi Isma'ila Haniyya a matsayin magajin Khalid Mash'al.
(last modified 2018-08-22T11:30:04+00:00 )
May 06, 2017 13:30 UTC
  • Palasdinu: Isma'ila Haniyya Ya Zama Shugaban Ofishin Siyasa Na Kungiyar Hamas.

A jiya Juma'a ne kungiyar ta Hamas ta zabi Isma'ila Haniyya a matsayin magajin Khalid Mash'al.

A jiya Juma'a ne kungiyar ta Hamas ta  zabi Isma'ila Haniyya a matsayin magajin Khalid Mash'al.

Kamfanin dillancin labarun "Kudsuna"  da ya bada labarin ya ci gaba da cewa; duk da cewa an kammal zaben na Isma'ila Haniyya a matsayin magajin Khalid Mash'al na shugabancin ofishin siyasa na kungiyar Hamas, amma sai ranar 15 ga wannan watan na Mayu za a sanar.

Ana kuma sa ran cewa  za a zabi Khalid Mash'al a matsayin shugaban majalisar shawara ta kungiyar Hamas. 

A yau asabar ne ake sa ran cewa kungiyar ta Hamas, za ta ci gaba da gudanar da zaben manyan jagororanta.