Palasdinu: Sojojin Sahayoniya Sun Kame Palasdinawa Da Dama.
(last modified Tue, 09 May 2017 12:38:01 GMT )
May 09, 2017 12:38 UTC
  • Palasdinu: Sojojin Sahayoniya Sun Kame Palasdinawa Da Dama.

Sojojin na Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame palasdinawa 15 a yammacin kogin jordan.

Majiyar Palasdinawa ta ce; Adaidai lokacin da  yajin cin abincin fursunonin palasdinawa ya shiga kwanaki ashirin da uku, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame wasu palasdinawan goma sha biyar a yammacin kogin Jorda.

A kowace rana ta Allah, sojojin haramtacciyar Kasar isra'ila suna kame palasdinawa a cikin yankuna daban-daban.  Kawo ya zuwa yanzu dai da akwai  palasdinawa 500 da su ke a cikin gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila.

A gefe daya, yahudawa 'yan share wuri zauna, sun kai wa palasdinawa hari a cikin unguwar "sha'afad, da ke tsakiyar birnin kudus. manufar kai harin dai shi ne tilastawa palasdianwa ficewa daga cikin yankin.