Palasdinu: Sojojin Sahayoniya Sun Kame Palasdinawa Da Dama.
Sojojin na Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame palasdinawa 15 a yammacin kogin jordan.
Majiyar Palasdinawa ta ce; Adaidai lokacin da yajin cin abincin fursunonin palasdinawa ya shiga kwanaki ashirin da uku, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame wasu palasdinawan goma sha biyar a yammacin kogin Jorda.
A kowace rana ta Allah, sojojin haramtacciyar Kasar isra'ila suna kame palasdinawa a cikin yankuna daban-daban. Kawo ya zuwa yanzu dai da akwai palasdinawa 500 da su ke a cikin gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila.
A gefe daya, yahudawa 'yan share wuri zauna, sun kai wa palasdinawa hari a cikin unguwar "sha'afad, da ke tsakiyar birnin kudus. manufar kai harin dai shi ne tilastawa palasdianwa ficewa daga cikin yankin.