Palasdinu: Wani Matashin Bapalasdine ya yi Shahada
Matashin ya yi shahada ne bayan da sojojin 'yan sayahoniya su ka harbe shi a gabacin birnin Kudus, a yau litinin.
Matashin ya yi shahada ne bayan da sojojin 'yan sayahoniya su ka harbe shi a gabacin birnin Kudus, a yau litinin.
Tashar telbijin din Sky News ta riya cewa matashin ya yi kokarin kai hari akan wani dan sanda ne, a lokacin da aka harbe shi.
Sau da yawa jami'an tsaron 'yan sahayoniya kan harbe palasdinawa maza da mata bisa riya cewa suna kokarin kai hari da wukake.
A gefe daya, a garin Kalandiya, an yi taho mu gama atsakanin matasan Palasdinawa da su ke goyon bayan fursunonin da su ke yajin cin abinci a gidajen kurkuku, da kuma jami'an tsaro 'yan sahayoniya.
Tun a ranar asabar ne dai palasdinawan su ka fara yin Zanga-zanga a yankuna daban-daban domin nuna goyon baya ga palasdinawan da su ke yin yajin cin abinci.