Samar Da Kasashe Biyu Shi ne Kawai Mafita- Abbas
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i20642-samar_da_kasashe_biyu_shi_ne_kawai_mafita_abbas
Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya sake nanata bukatar samar da kasashe biyu a yankin Gabas ta tsakiya wanda hakan ne a cewarsa zai bada damar samar da kasar Palasdinu mai cin gashin kanta.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
May 23, 2017 11:19 UTC
  • Samar Da Kasashe Biyu Shi ne Kawai Mafita- Abbas

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya sake nanata bukatar samar da kasashe biyu a yankin Gabas ta tsakiya wanda hakan ne a cewarsa zai bada damar samar da kasar Palasdinu mai cin gashin kanta.

Mista Abass ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da shugaba Donald Trump na Amurka dake ziyara a yankin.

Saidai a cewar labarin Mista Trump ya kauda kai akan wannan kiran, amman ya ce zai yi duk iaya kokarinsa na ganin an samu zamen lafiya tsakanin Palasdinu da Israíla.

Shuagba Donald Trump dake ci gaba da ran gadinsa na farko a yankin bai fayyace hanyoyin da zai bi ba wajen samar da zamen lafiya tsakanin bangarorin biyu ba.