Mahukuntan Bahrein Sun Yi Wa Ayatullahi Shekh Isa Kasim Daurin Talala
Ma'aikatar cikin gida ta kasar Bahrein ta sanar da cewa Dakarun tsaron kasar sun kai farmaki gidan babban malamin Addinin nan mabiyin mazhabar Shi'a Ayatullahi Shekh Isa Kasim, bayan kwashe ayoyi na taho mu gama da mabiyansa , an kame wasu daga cikin mabiyan tare da yi masa daurin talala.
Tashar telbijin din Al'alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto majiyoyin kasar Bahrein na cewa a wannan Talata Dakarun tsaron kasar sun kai farmaki gidan babban malamin Addinin nan mabiyin mazhabar Shi'a Ayatullahi Shekh Isa Kasim, bayan kwashe ayoyi ana taho mu gama da mabiyansa , an yi awan gaba da matasa kimanin 150 daga cikin mabiyan nasa, saidai Ma'aikatar cikin gidan kasar ta bayyana cewa Matasa 50 ne kacal aka kame kuma mafi yawan su daga cikin mutanan da ake Jami'an tsaron kasar ne ke nema ruwa a jallo wadanda suke tsere daga gidan kaso na Jau.
A bangare guda Shugaban Cibiyar kare hakin bil-adama ta kasar Bakir Darwish ya bayyana cewa Al'ummar kasar Bahrein sun dora alhakin wannan mumunar siyasa da taken hakin 'yan kasar da mahukuntar kasar ke yi kai tsaye a kan kasashen Amurka, Birtaniya, Saudiya da hadaddiyar daular Larabawa.
A nasu Bangare Maliman Addinin Musulinci na kasar Labnon sun kira taron manema labarai kan halin da ake ciki a kasar ta Bahrein tare da kiran Al'ummar kasar da su fito kan tituna domin kare babban Malamin Shekh Isa Kasim.
Har ila yau sanarwar tayi alawadai kan yadda kasashen Duniya suka shuru dangane da halin da Al'ummar kasar Bahrein din ke ciki,sannan kuma sun bayyana goyon bayan su ga babban malamin sheikh Isa Kasim da kuma Al'ummar kasar.
A ranar Lahadin da ta gabata ce wata Kotu a kasar ta Bahrein ta yankewa Shekh Isa Kasim Hukuncin daurin talala na shekara guda tare da kwace dukkanin dukiyar sa , lamarin da ya janyo fishin mafiyansa tare da nuna rashin amincewar su da wannan hukunci na zalinci.