Bahrain: Jami'an Tsaro Na Ci Gaba Da Cin Zarafin Jama'a
(last modified Thu, 25 May 2017 06:59:16 GMT )
May 25, 2017 06:59 UTC
  • Bahrain: Jami'an Tsaro Na Ci Gaba Da Cin Zarafin Jama'a

Jami'an tsaro gami da daruruwan 'yan banga na ci gaba da killace gidan babban malamin addini a kasar Bahrain Sheikh Isa Kasim, da kuma ci gaba da cin zarafin jama'a a da suke nuna rashin amincewa da haka a fadin kasar

Shafin yada labarai na jaridar Manama Post ya bayar da rahoton cewa, daruruwan motoci masu sulke na jami'an tsaro tare da daruruwan 'yan banga na masarautar kama karya ta Al Khalifa, suna ci gaba da killace gidan Ayatollah Sheikh Isa Kasim, bayan da suka kashe wasu daga cikin masu zaman dirshan a wurin, da kuma jikkata daruruwa, da kuma kame wasu daruruwan na daban.

Har yanzu dai babu wani wanda ya san halin da malamin yake ciki, kamar hatta iyalansa ba su san inda yake ba, yayin da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suke ci gaba da yin tir da Allah wadai da wannan mummunan aiki na masarautar kasar.

A nata bangaren majalisar dinkin duniya ta yi kira da a gudanar da binciken gaggawa a kan kisan gillar da jami'an tsaron masarautar suka yi wa jama'a a kofar gidan Sheikh Isa Kasim.

Harin na jami'an tsaron Bahrain a kan gidan shehin malamin ya zo ne kwana daya bayan kammala tattawar da sarkin kasar ya yi ne da Donald Trump da kuma sarkin Saudiyya a Riyadh.

Masarautar bahrain dai tana zargin Sheikh Isa Kasim da karbar kudaden zakka da Khumusi da mabiyansa ke aika masa da su ba tare da ya karbi izinin yin hakan daga masarautar ba, ida masarautar ta bayyana hakan a matsayin halasta kudaden haram.

Mafi yawan jami'an tsaron masarautar Bahrain dai 'yan kasashen Pakistan, da Jordan ne, domin kada a dauki 'yan asalin kasar wadanda mafi yawansu mabiya mazhabar shi'a ne wadanda masautar take ta kokarin danne su.