Iyalan Wadanda Mahukuntan Bahrain Ke Tsare Da Su Na Cikin Damuwa
Iyalan mutanen da mahukuntan Bahrain suka kama Durraz na cikin damuwa saboda rashin sanin makor danginsu.
A zantawar da da jaridar Wasat ta kasar Bahrain ta yi da iyalan mutanen da masarautar kasar ta kame a garin Durraz, sun nuna damuwa matuka a kan rashin sanin halin da danginsu suke ciki.
Jami’an tsaron masaratar Bahrain tare da ‘yan banga na wannan masarauta, sun kaddamar da farmaki da manyan makamaia a unguwar Durraz da ke kusa da birnin mana, domin tarwatsa jama’a da suke zaman dirsha a kofar gidan babban malamin addini na kasar.
Jami’an tsaron tare da ‘yan banga sun kame mutane 286 wadanda a ‘yan kwanakin bayana jin duriyar inda wasu daga cikinsu suke inda ake tsare da su, amma a halin yanzu babu duriyar ko daya daga cikinsu, lamarin da ya kara tayar da hankulan danginsu.