Kasar Maroko Ta Bukaci Bunkasa Alaka Da Kasar Qatar
(last modified Mon, 26 Jun 2017 13:06:45 GMT )
Jun 26, 2017 13:06 UTC
  • Kasar Maroko Ta Bukaci Bunkasa Alaka Da Kasar Qatar

Sarkin kasar Maroko ya bayyana cewa: Kasarsa tana bukatar bunkasa alaka da taimakekkeniya da kasar Qatar.

A wani sako na musamman da Sarkin kasar Matoko Muhammad na Shida ya aike wa takwaransa na Qatar Tamim bin Hammad Ali-Sani yana dauke da bukatar neman fadada alaka a tsakanin kasashensu a bangarori da dama.

Wannan bukata ta Sarkin kasar Maroko ta zo ne a daidai lokacin da kasar Qatar take cikin halin tsaka mai wuya sakamakon hade baki da kasashen Larabawan yankin tekun Pasha suka yi a kanta ta hanyar yanke alakar jakadanci da ita tare da kokarin maida ita saniyar ware karkashin jagorancin kasar Saudiyya.

A ranar 5 ga wannan wata na Yuni ne kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain gami da Masar suka sanar da yanke alakar jakadanci da kasar Qatar bisa zargin goyon bayan ayyukan ta'addanci musamman goyon bayan kungiyoyin gwagwarmaya irin kungiyar Hamas, kungiyar Hizbullahi da kuma kungiyar Ihwanul-Muslimin na Masar.