Dubban 'Yan Gudun Hijiran Siriya Sun Fara Dawowa Gidajensu
(last modified Sat, 01 Jul 2017 05:43:44 GMT )
Jul 01, 2017 05:43 UTC
  • Dubban 'Yan Gudun Hijiran Siriya Sun Fara Dawowa Gidajensu

Hukumar Kolin Kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: 'Yan gudun hijiran Siriya fiye da rabin miliyan ne suka koma muhallinsu a cikin wannan shekara ta 2017.

Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma'a ta sanar da cewa: Bayan samun nasarar kyautata al'amura musamman wanzuwar zaman lafiya a wasu yankunan kasar Siriya 'yan gudun hijiran kasar fiye da 500,000 ne suka koma muhalinsu da suke garuruwan Halab, Homs, Hamah da wasu yankuna da suke gefen birnin Damasqas fadar mulkin kasar.

Tun bayan bullar rikicin kasar Siriya a ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2011 miliyoyin al'ummar Siriya ne suka tsere daga muhallinsu, inda fiye da 440,000 suka samu mafaka a sassa daban daban a cikin kasar ta Siriya, yayin da wasu fiye da 5,000,000 suka tsere zuwa kasashen makobta irin Turkiyya, Lebanon, Iraki, Masar da sauransu.