Tattaunwa A Tsakanin Tawagar Hamas Da Mahukuntan Kasar Masar.
(last modified Thu, 06 Jul 2017 18:58:02 GMT )
Jul 06, 2017 18:58 UTC
  • Tattaunwa A Tsakanin Tawagar Hamas Da Mahukuntan Kasar Masar.

Gwamnatin kasar Masar ta sanar da cewa ganawar da tawagar kungiyar Hamas ta yi armashi sosai, kuma za ta taimaka wajen warware matsalolin mutanen Gaza.

Gwamnatin kasar Masar ta sanar da cewa ganawar da tawagar kungiyar Hamas ta yi armashi sosai, kuma za ta taimaka wajen warware matsalolin mutanen Gaza.

Ita ma kungiyar ta Hamas ta ce muhimmin abinda ta sanya a gaba shi ne kawo karshen sabanin da ya ke a tsakanin bangarorin Palasdinawa.

Bugu da kari tawagar ta Hamas ta bayyana amincewarta da kasantuwar Masar mai shiga tsakani domin warware sabanin da ya ke bangarorin palasdinawa.

Wani sashe na bayanin kungiyar ta Hamas ya kunshi yin kira ga shugaban gwamnatin kwrya-kwaryar palasdinu Mahmud Abbas Abu Mazin da ya kafa kwamitin da zai binciki halin da mutanen Gaza su ke ciki.