An 'Yanto Tsohon Garin Mausil
(last modified Sat, 08 Jul 2017 11:56:12 GMT )
Jul 08, 2017 11:56 UTC
  • An 'Yanto Tsohon Garin Mausil

Komandan dakarun hadin gwiwa na yaki da kungiyar ISIS a Iraki ya bayyana cewa an tsarkake bangaren tsohon garin Mausil daga 'yan ta'addar ISIS

Tashar Telbijin din Almayadeen ta habarta cewa a mahangar tsaro dakarun tsaron kasar Iraki sun kwace Tsohon garin Mausil, abinda ya rage a hanun mayakan na ISIS wata sukurwa ce daidai kofar shigar Dajla dake gabashin yankin Almaidan.

A bangare guda Dakarun tsaron kasar Irakin sun dakile wani kutse da 'yan ta'addar suka yi kokarin yi daga gabar yammaci zuwa gabar gabashin garin na Mausil, inda suka hallaka 'yan ta'addar ISIS din 35 tare da jikkata wasu 6 na daban.

Tun a ranar 24 ga watan Janairun wannan shekara ta 2017 da muke ciki 'yan ta'addar ISIS din suka mamaye bangaren gabashin garin na Mausil, kuma a ranar 19 ga watan Favrayun da ya gabata ne aka fara kai farmakin tsarkeke yankin, inda aka kamala shi a ranar 29 ga watan yunin da ya gabata.