An Zargi Masarautar Kasar Bahrain Da Cin Zarafin 'Yan Kasa
Babbar cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain ta zargi mahukuntan kasar da cin zarafin bil adama da kuma take hakkokin 'yan kasa.
A cikin wani bayani da babbar cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain ta fitar a jiya a cikin shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa masarautar Bahrain tana yin amfani da salon a kama karya domin rufe bakunan al'ummomin kasar a kan ta'asar da take tafkawa.
Bayanin cibiyar ya ce, masarautar kasar ta yi amfani da hanyoyi daban-daban da suka saba wa doka wajen cin zarafin 'yan kasa masu hakki a kan dukaknin sha'anin da ya danganci kasarsu, da hakan ya hada da kashe su da kuma kame su da azabtar da su a gidajen kaso saboda bayyana ra'ayoyinsu na siyasa.
Cibiyar ta yi kakkausar suka dangane da salon siyasar munafunci da kasashen turai suke nunawa a kan batun kare hakkin bil adama, dangane da yadda suka yi gum da bakunansu a kan kisan da ake yi wa al'ummar Bahrain saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba, ba tare da wata kasar turai ta ce uffan ba kan hakan, saboda alaka da kuma maslaha da ke tsakaninsu da masarautar ta Bahrain.